Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA -Karen Andrews, sakatariyar harkokin cikin gida ta kasar ta ce "manufofin Hamas da kungiyoyin masu tsattsauran ra'ayi ba su da wurin zama a Ostiraliya.
Ta kara da cewa yana da mahimmanci dokokinmu su maida hankali kan ayyukan ta’addanci da kuma ‘yan ta’addan, amma kuma yana da kyau mu hada har da wadanda ke shiryawa da tallafawa da aikata ayyukan ta’addancin.
Kungiyar Hamas da ke iko da zirin Gaza ta na gwagwarmya ne domin ‘yantar da Kudus, kuma ta sha shiga yaki da Isra’ila.
342/